Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa, Saleh Mustapha wanda kwamandan kungiyar Boko Haram ne ya tuba ya mika wuya ga jami’an tsaro.
Kakakin Hedikwatar, Bernard Onyeuko ne ya bayyanawa manema labarai haka a Abuja inda yace Mustapha ya mika kansa a Bama, jihar Borno wanda hakan ba karamar nasara bace.
Hakanan ya kara da cewa akwai jimullar 51,114 na Boko Haram da iyalansu da suka mika wuya suka tuba.