Hukumar yan sandan jihar Anambra tayi nasarar cafke wani mutumin daya yi yunkurin yiwa ‘yar aikinsa fyade a babban birnin jihar, Awka.
Yarinyar yar shekara 12 ta fado daga gidan sama domin ta gujewa lalata da uban gidan nata, wanda hakan yasa ta karye a kafafuwanta.
Kuma hukumar yan sanda sun bayyana cewa sun kama mutumin yayin da suke cigaba da gudanar da binxcike akan lamarin.