fbpx
Sunday, December 4
Shadow

‘Yar Gidan Tukur S. Tukur (Dandugaji) Ta Bata

Tsohon tauraron fina-finan Hausa daya fi kwarewa a harkar barkwanci, Tukur S. Dan dugaji ya sanar da bacewar diyarshi me suna Shukra, Dandugaji ya fitar da wata sanarwa ta dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda ya bayyana cewa tun daga makarantar Isilamiya aka nemeta aka rasa, haka kuma ya kara da cewa tana da ciwon jinnu wanda dama sun taba dauketa.

Gadai sakon daya fitar din kamar haka:

“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJ’IUN.

JAMA’A WANNAN YARINYAR DA KUKE GANI SUNANTA SHUKRA (AISHA TUKUR S TUKUR), ITA CE ‘YA TA TA FARI, YANZU DA MISALIN KARFE 2:30 na yammar nan AKA NEMETA AKA RASA DAGA MAKARANTAR ISLAMIYYA, TANA SANYE DA FARIN HIJAB DA RIGA DA WANDON MAKARANTA KALAR RUWAN TOKA, AKWAI NIKAF DA MEDICAL GLASS A FUSKAR TA MAI JAN FRAME, TANA DA LALURAR ALJANU DA SUKA TABA DAUKE TA, WANNAN SHINE KARO NA BIYU,

Karanta wannan  YANZÚ-YANZÚ: Amìnu Muhammad Zaí Samú Kúlawa Ta Músamman Kai Tsayé Daga Gidaúniyar A'isha Buharí

IDAN ALLAH YA SA ANGANTA A KIRAWO 08060228130.

ALLAH YA BAYYANA MIN ITA. JAMA’A A TAYA NI DA ADDU’A AKAN SHUKRA TA.”

Muna fatan Allah ya bayyanata ya kuma bata lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *