fbpx
Friday, February 26
Shadow

‘Yar Najeriya, Farida Mustapha da ta samu maki mafi kyawu a jami’ar kasar Rasha

Farida Mustapha,  ‘yar Najeriya da ta je karatu jami’ar kasar Rasha, ta kammala da maki mafi kyawu na 5.0 CGPA.

 

Ta kammala karatun digirinta daga jami’ar Kuban State University of Technology,  Rasha a tsangayar Kimiyyar Man Fetur.

 

A hirarta da Punch ta bayyana cewa tana aji na 2 a jami’ar ABU Zaria ta ga tallar daukar nauyin karatu zuwa kasar waje kuma ta nema. Cikin ikon Allah sai ta Samu amma sai gashi ya fito a matsayin karatun Injiniyan man fetur ce zata yi, maimakon karatun likita da take son yi.

 

Tace an sha dambarwa, dan kuwa mahaifinta ya ce ba zata je ba, hakanan yayanta ma yace ba zata je ba saboda ba karatun likita bane. Saidai mahaifiyarta ta bata goyon baya.

 

Tace daga karshe dai bayan data yi bincike aka bayyana mata cewa zata iya canja karatun nata idan ta je, Mahaifinta ya Amince da lamarin. Saidai bayan da suka je, suka kammala karatun koyan yaren kasar Rasha sai aka gaya mata cewa ba zata iya canja kwas din nata ba. Da ta gayawa mahaifinta, yace hakka Allah yaso, inda ta ci gaba da karatun har ta kammala.

A yanzu kuma ta sake samun wata damar daukar nauyin karatun inda take karatu a kasar Ingila na digirinta na 2. Ta bayyana cewa idan ta kammala zata so ta yi aiki a bangaren da ta yi karatun.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *