fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Matashiya mai gyaran gashi ta daba wa saurayinta wuka kan batan N1500

Rundunar ‘yan sanda reshen Bayelsa ta cafke wata mai gyaran gashi yar shekaru 28 mai suna, Ebiere Ezekiel wacce ake zargi da daba wa saurayinta dan shekaru 21 mai suna, Godgift Aboh wuka har lahira kan kudi.

Lamarin ya faru ne a inda suke zama da ke Obele, karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa yayin takaddama kan bacewar N1,500.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Mike Okoli, ya tabbatar faruwar lamarin tare da kame wacce ake zargin a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu, an ce ta dade tana soyayya da mamacin sama da watanni 12.

An bayyana cewa rikicin ya fara ne lokacin da mamacin ya mari Ebiere saboda ta tambaye shi kan bata kudin.

Ana cikin rikicin sai ta dauki wuka, ta daba masa a ciki kuma daga baya ya mutu.

A yanzu haka ana kan gudanar da bincike kafin a tura fayil din zuwa kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *