Yara biyu da ba a tantance su ba sun rasa ransu a ranar laraba bayan da suka makale cikin wani gini da ya rushe a yankin Gafari Balogun na Ogudu, jihar Legas.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce ginin ya rushe ne sakamakon laka wanda ta samu sakamakon ruwan sama mai karfi.

Ya ce wadanda abin ya shafa yara ne, kuma an gano gawawwakinsu.
Ya ce, “Kungiyar ta samu kira ne da karfe 12:30 na dare game da rushewar wani gini mai hawa daya a titin Gafari Balogun a Ogudu.
“Lokacin da aka isa wurin da abin ya faru, masu ba da rahoto na hukumar sun lura cewa ginin ya rushe ne sakamakon laka a bayan ginin wanda ruwan sama mai karfi ya haddasa.
An sanar da jami’an cewa yara biyu, namiji da mace sun makale kuma nan da nan aka fara aikin ceton. Abin takaici, an sami gawawwakinsu ne kuma an kwashe gawawwakin zuwa gurin aje gawa.
“Za ayi gwajin amincin a sauran ginin da yanzu haka ya lalace kuma an kebe shi.”