Rahotanni daga jam’iyyar APC na cewa, Yariman Bakura da gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar sun janye daga neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Lamarin ya farune bayan ganawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ‘yan takarar jam’iyyar APC din a fadarshi da yammacin jiya.
Shugaban kasar ya nemi ‘yan takarar su je su sasanta kansu.