Wani yaro dan shekara 12 ya kashe mahaifiyarsa, Ayobiyi Cook ‘yar Najeriya a Alabama dake kasar Amurka.
Yaron daga farko ya bayyanawa hukumar ‘yan sanda cewa bashi ne ya kasheta ta be wani barawo ya shigo gidan ya kasheta ya gudu.
Amma bayan hukumar ta zurfafa bincike ya fada masu gaskiyar abinda ya faru cewa shine ya kasheta bisa hadari bada saninsa ba.
A halin yanzu dai zasu je kotun su a gudanar da shari’ar amma yaron zai cigaba da zama a hannun ‘yan uwan nasa kuma magaifinsa dan sanda ne a Birmingham.