Yaron da hanjinsa ya ɓace a asibitin Legas ya mutu
Wani yaro ɗan shekara 12, mai suna Debola Akin-Bright, wanda a baya aka bayar da rahoton ɓacewar ƴan hanjinsa a asibiti, ya rasu.
Ɗaya daga cikin iyalan yaron ne ya tabbatar wa BBC da hakan, inda ya ce kafin mutuwarsa, yaron ya yi fama da zuban jini a cikin tumbinsa.
Ya ce iyalin sun garzaya da yaron ne zuwa asibiti, inda aka zarce da shi wurin bayar da kulawa ta musamman na Asibitin Koyarwa na Jami’ar jihar Legas, inda a can ne rai ya yi halinsa.
Tun farko yaron dai ya shiga matsanancin hali bayan jerin tiyata da aka yi masa a baya, inda a nan ne aka tabbatar da cewa babu wani ɓangare na hanjinsa.
A tattaunawar da ta yi da BBC, a farkon watan Satumba, mahaifiyar yaron, Mrs Deborah Akin-Bright, ta ce ta kasa gane yadda za a ce hanjin ɗanta ya ɓace kuma ba a san wanda ya ɗauka ba.
A cikin tattaunawar, ta ce tun farko an kai yaron wani asibiti ne mai zaman kansa bayan ya fara amai tare da gudawa na kwana biyu.
Sai dai bayan kula da shi na kimanin kwana biyu ba tare da samun sauƙi ba, an yi wa yaron hoton ciki, inda aka gano cewa yana fama da cutar tsakuwar hanji (Appendicitis), da fashewar hanji.
Inda bayan yin hoto na biyu aka ƙara gano cewa yana kuma fama da toshewar hanji.
Wannan lamari ne ya sa aka gudanar da tiyata ba tare da ɓata lokaci ba.
Sai dai bayan yin tiyata har sau biyu a asibitin mai zaman kansa, jikin Debola ya ci gaba da rincaɓewa, inda iyayensa suka lura cewa wani abu na ɗiga a cikin cikinsa, lamarin da ya tursasa wa iyayen ɗaukan shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar jihar Legas.
A cikin kwanankin farko bayan kai yaron Asibitin koyarwa, lamarin nasa ya ci gaba da dagulewa, inda wurin da aka yi aiki na farko ya fashe, kuma ruwa ya ci gaba da tuɗaɗowa.
Daga nan ne aka yanke shawarar yi wa yaron wata tiyatar.
Sai dai bayan buɗe cikinsa likitoci sun shaida wa iyayen cewa ba su ga ƙaramin ƴaƴan hanji na yaron ba, kuma akwai yiwuwar cewa sun ɓace ne a asibitin farko.
Mrs Debora ta ce “a lokacin da likita ke yi min bayanin ɓacewar ƴaƴan hanjin na kasa fahimtar me yake nufi, na shafe kwanaki ina tunanin cewa ƙarya suke yi, ta yaya za a ce babu hanji a cikin mutum?”
Ta ƙara da cewa “na sharɓi kuka kamar zan mutu, ta yaya wannan yaro zai rayu babu hanji?”
Bayan ɓullar labarin ɓacewar hanjin yaron ne gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ziyarci yaron, tare da yin alƙawarin ɗaukar nauyin kula da shi.
Bugu da ƙari ita ma Majalisar Dokokin jihar Legas ta kafa wani kwamiti domin yin bincike kan ɓacewar ƴaƴan hanjin marigayin.
Likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar jihar Legas sun dage kai-da-fata kan bayaninsu na rashin ganin ƴaƴan hanji a cikin yaron, kuma sun ce suna da bidiyon tiyatar da suka yi, wanda ke zaman shaidar cewa babu hanjin a lokacin da suka buɗe cikin marigayi Debola.