fbpx
Saturday, June 10
Shadow

“Yau Buhari gobe Atiku: Ba haka ake siyasa ba”>>Wasu suka gayawa Rashida Mai sa’a bayan an ganta da atamfa me dauke da hoton shugaba Buhari

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa kuma me baiwa gwamnan jihar Kano shawara a harkokin mata, Rashida Adam Abdullahi wadda akewa lakabi da mai sa’a kenan a wannan hoton nata tare da wasu mata inda suke sanye da atamfa me dauke da hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da alama sun saka kayanne dan murnar ziyarar da shugaban kasar ya kai jihar a satin daya gabata.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

To saidai bayan ta saka wannan hoton nata a dandalinta na sada zumunta da muhawara, wasu sun yi Allah wadai da irin yanda ba’a san dan siyasar da take so ba tsakanin Shugaba Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar daya canja sheka zuwa PDP, sun rika fadin cewa “yau Buhari gobe Atiku d ba haka ake siyasa ba”.

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Gadai wasu daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana akan wannan hoton.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *