fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Yau Shaikh Dahiru Bauchi ke Sallar Idi

Da safiyar ranar Asabar ne ake sa ran Shahararren malamin Mususluncin nan Shaikh Dahiru Usman Bauchi zai yi Sallar Idi, sabanin ranar Lahadi Sarkin Musulmi ya ba da umarni a yi.

 

 

Hakan dai ya biyo bayan jawabin da malamin ya yi ne cewa ya samu bayanan da suka tabbatar masa an ga wata a wurare daban-daban a Najeriya ranar Juma’a.

Ganin jama’a masu yawa

A cewar Shaikh Dahiru Bauchi, dukkan sharuddan da ake bukata don ajiye azumi sun tabbata.

 

 

“Da ma hukuncin da aka ba mu shi ne wata yana tabbata in aka samu mutane adilai guda biyu sun ce sun ga wata kuma an tabbatar da adalancinsu, ko ko jama’a masu yawa”, inji malamin.

 

 

“Jama’a masu yawa inda take farawa daga an samu mutum biyar baligai masu hankali, to shi ke nan an samu jama’a mustafidah – su kuma ba a binciken adalcinsu.

 

 

“A nan cikin garin Bauchi mutum takwas sun gani. A Liman Katagum mutum 10 sun gani – faya kam ma yaron gidanmu ne.

 

 

“Mun samu labari a Geidam, Yobe ke nan, mutane da yawa sun ga wata; mun samu labarin wasu sun kai labarin sun ga wata gidan Shehu Gibirima wajen halifansa.

 

 

“Jama’ar Zariya sun aiko mana sun ce sun ga wata, labari ya same mu an ga wata a Yawuri da Zariya.

 

 

“Tun da jama’a da yawa sun gani a garuruwa da dama, ba maganar mutum biyar ba, kuma Allah Ya wajabta mana azumi Ya ce ‘yan kwanaki ne… to yau wannan watan ya kare”, inji shehin malamin.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Shugaban karamar hukumar mahaifar Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar NNPP

 

 

‘Ba mu samu labari da wuri ba’

Ya kuma kara da cewa ya samu labari an sanar da Sarkin Zazzau, wanda shi kuma ya sanar da Sarkin Musulmi, amma jagoran al’ummar Musulmin na Najeriya ya ce ya riga ya sanar cewa ba a ga wata ba.

 

 

“Da mun samu labari sahihi da wuri, da sai mu dage mu gaya wa Sarkin Musulmi ya yi magana a rediyo; to ba mu samu labari da wuri ba…”

 

 

Bisa wadannan dalilai ne mabiyan Shaikh Dahiru Bauchi suka ce za su yi Idi ranar Asabar.

 

 

“Dogaro da wadannan hujjoji, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Allah Ya yarda da shi),  ya umarci sauran almajirai da muridai da sauran jama’a cewa ranar Asabar ce 1 ga watan Shawwal”, inji wani makusanci ga malamin, wanda ya kara da cewa, “domin ai babu da’a ga wani mahaluki cikin saba wa Ubangiji”.

 

Da misalin karfe 12.15 na daren Juma’a ne dai Shaikh Dahiru ya bayyana matsayinsa yana mai cewa “labari ya zo mana sahihi an ga watan Shawwal, [don haka] gobe za a tashi da Idi, babu azumi tun da watan Ramadana ya kare yau [Juma’a]

 

 

Tuni dai mabiyan shehun malamin suka yada sanarwa ga sauran ‘yan Darikar Tijaniyya da cewa a ajiye azumin Ramadan shekarar 1441 bayan hijira.

 

 

“Daga Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bayan kammala bincike da tantancewa, ya tabbata ‘yan uwa da dama sun ga watan Shawwal”, inji sanarwar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.