Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Tau wa’adin jam’iyar APC ke cika na rufe siyar da kaf fom din tsayawa takarar neman kujeru daban-daban a cikin Nijeriya.
Kamar yadda jam’iyar APC ta sanar a kwanakin baya na rufe siyar da fom din tsayawa takara a kujeru daban daban inda jam’iyar ta ce ta siyar da fom sama da dubu daya a cikin tarayyar Nijeriya.
Jam’iyar tace ta siyar da fom din takarar kujerar shugaban kasa 26 na gwamnonin jihohi 109 na yan Majalisun Dattawa 270 na yan Majalisun wakilai 9960 inda mataimakin sakataren jam’iyar yace zasu sanar da matsayar jam’iyar na rufe siyar da fom din tsayawa takara ayau ko kuma karin wa’adin siyar da fom din.