fbpx
Monday, June 27
Shadow

Yaushe Gwamnati Za Ta Hana Kisan ‘Yan Arewa A Ƙasar Inyamurai?>>Matasan Arewa A Kudu

Gamayyar ƙungiyoyin Matasan Arewa da ke Kudancin Nijeriya ta ƙalubalanci Gwamnatin Tarayya a kan yaushe ne za ta dakatar da kisan gilla da ake wa ‘yan arewa mazauna kudancin ƙasar nan musamman a yankin Inyamurai da ke kudu maso gabashin ƙasar.

Matasan sun bayyana haka ne yayin da suke bayyana takaicinsu a kan kisan da aka yi wa wata mata ‘yar arewa tare da ‘ya’yanta huɗu da wasu mutum shida dukkansu ‘yan arewa a Jihar Anambara a cikin makon nan.

Da yake ƙarin haske ga LEADERSHIP Hausa a farkon makon nan, Shugaban Gamayyar Matasan, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya bayyana cewa ba domin ‘yan arewa mutane ne masu bin doka da son zaman lafiya ba, da yanzu ƙasar ta hargitse saboda irin kisan mummuƙen da ake musu.

“Wai sai yaushe ne Gwamnatin Shugaba Buhari za ta hana kisan da ake wa mutanenmu na arewa a yankin kudu musamman a ƙasar Inyamurai. Ko a makon nan an kashe wata ‘yar arewa da take zama a Orumba South da ke Jihar Anambara tare da ‘ya’yanta su huɗu. Akwai kuma wasu sojoji da suka taso daga Kaduna suka je ɗaurin aure a Anambara waɗanda su ma an kashe su a can. Sannan akwai ƙarin wasu mutum shida da su ma aka kashe dukkansu ‘yan arewa a Anambara. Yanzu in da ‘yan arewa ne suka aikata wannan aika-aika da ka ji ko ina ya ɓarke da tofin Allah-tsine kuma a nemi a bi musu hakkinsu. Me ya sa mu idan hakan ta faru da mutanenmu su ma ba za a bi musu hakkinsu ba. Rai ya fi rai ne? Me aka mayar da ‘yan arewa ne a ƙasar nan da har za a riƙa zubar da jininsu a banza?

“Muna kira da gwamnati ta sake tunani dangane da halin da ‘yan ƙasa suke ciki domin babu waɗanda suka kai `yan arewa haƙuri, tun daga 1999 ake yi mana kisan gillah har zuwa yanzu 2022 ba a daina ba, a kashe mana jami’an tsaro da fararen hula ba su ji ba, ba su gani ba. Ya kamata a kawo ƙarshen wannan wulaƙancin domin jinin ɗan arewa ba wai a banza yake ba, abin ya isa haka.” In ji shi.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Gwmamna Uzodimma ya gargadi 'yan bingar jihar Imo su bar jihar nan da kwanaki goma kafin zuwan shugaba Buhari

Ya nemi gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin ta magance lamarin domin ganin abin da ke faruwa bai haifar da tashin-tashina a wasu yankuna na ƙasar ba.

Da ƙungiyar take nuna takaicinta a kan shirun da shugabannin arewa ke yi kan waɗannan miyagun abubuwa da ke faruwa da mutanensu, ta ce a gaskiya matasan arewa ba za su lamunci ɗora musu shugabannin da ba za su iya kare rayuka da dukiyoyinsu ba.

“Dangane da shugabannin arewa masu madafun Iko, muna musu gargaɗi da jan kunne sannan muna kira gare su da babbar murya, wallahi su sani mun daina bari a dinga cutar damu ta hanyar ɓatagarin shugabanni, dole a bari mutane su samar wa kansu shugabannin da za su nuna kishi a kansu.

“Haka nan idan har gwamnati tana son ɗorewar dimokaradiyya a Nijeriya to ta soke tsarin amfani da wakilai masu zaɓe (delegates) a yi zaɓe ƙato bayan ƙato saboda mulkin kama karyar ya yi yawa. Muna da ‘yanci a matsayinmu na ‘yan ƙasa, PDP sun yi mun gani, haka ma APC su ma sun yi mun gani, dan haka muke kira da a soke delegate, ba mu yarda da su ba”, in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.