fbpx
Friday, July 1
Shadow

Yawan mutanen da ake kashewa yanzu sun fi wanda aka kashe a yakin Basasa>>Edwin Clark

Dan siyasa kuma tsohon Ministan Labarai daga kudancin Najeriya, Edwin Clark ya bayyana cewa yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya a yanzu ya fi wanda aka kashe a lokacin yakin Basasa.

 

Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi da Sunnews.  Yace babu Dimokradiyya a Najeriya domin mulkin da ake yi a yanzu yama fi na Soja Muni.

Ya kara da cewa dan hakane ma suka kai gwamnati kara inda suke neman a biyasu Biliyan 50 a matsayin diyyar na daidai ba da aka aikata musu.

Karanta wannan  Fulani zasu dandana kudarsu domin masu daukar nauyinsu sun kusa sauka akan mulku, cewar haramtacciyar kungiyar IPOB

 

Da yake magana akan matsalar tsaro yace abubuwa kullun sai kara tabarbarewa suke, uace yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya a yanzu yafi wanda aka kashe a lokacin yakin basasa.

 

Yace ka duba kasar Amurka, mutum 1 ne aka kashe amma gaba daya hankula sun tashi amma a Najeriya sai a kashe mutum 100 amma gwamnati bata damu ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.