Ministan Lafiya, Osagie Ehanire Ya bayyana cewa yawan ‘yan Najeriya ne ke hana kasar ci gaba.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka kaddamar a Abuja inda yace yawan ‘yan kasar na sa a kasa samun ingancin rayuwa.
Yace a yanzu an yi kiyasin akwai mutane miliyan 214 a Najeriya kuma mata na haihuwar akalla ‘ya’ya 5.
Yace kuka wannan duk na faruwane saboda rashin bin tsarin kayyade iyali yanda ya kamata.