Monday, March 30
Shadow

Yawan sojojin Najeriya da Boko Haram ta kashe a harin kwantan bauna sun kai akalla 100

Rahitanni daga jihar Borno na kara bayyana kan harin kwantan bauna da Kungiyar Boko Haram bangaren ISWAP ta kaiwa sojojin Najeriya.

 

A rahoton farko wanda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito yace sojoji 70 ne suka mutu a harin.

 

Saidai a Rahoto  shahararren me kawo rahoto ka  rikice-rikice da ta’addanci a Najeriya, Ahmad Salkida ya saki, na cewa sojojin da aka kashe a kalla sun kai 100.

 

Salkida ta shafinshi na HumAngle ya bayyana cewa akwai kuma sojoji da dama da suka bace sanan wanda suka ji rauni a harin an garzaya dasu Asibiti.

 

A cikin sojojin da suka mutu, akwai kusan manayn sojoji guda 4. Akwai kuma mafarauta 4 da aka rutsa dasu a harin.

 

Sannan akwai sojoji da ba’a san iya yawansu ba da maharan suka yi garkuwa dasu

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *