Hukumar tabbatar da inganci kayayyaki a Najeria wato (SON) ta bayyana damuwa kan ƙaruwar shiga da kayayyaki marasa inganci a cikin ƙasar musamman na abinci.
Shugaban Hukumar Malam Farouk Ali Salim, ya shaida wa BBC cewa, wannan matsalace babba saboda a yanzu duk kasuwar da aka je a Najeriya, idan ka dauki kaya kashi 8 a cikin 10 duk suna da matsala.
Ya ce ko ta wajen tantance kayan ko kuma lokacin amfaninsu ya kare, wanda hakan kuma zai iya sa tattalin arzikin kasar ya gamu da cikas matuƙar gwamnati ba ta ɗauki matakin daƙile matsalar ba.
”Abin damuwar shi ne yadda ake shigo da kayan abinci barkatai ba tare da an tabbabar da ingancinsu ba” in ji shi.
Malam Farouk Ali Sali, ya ce,” Kamar misali a yanzu za ka ga kamfanonin da ke sayar da kayan gini suna rufewa saboda mutane na zuwa wasu kasashen su siyo irin kayan wanda suke marassa inganci, sabaoda haka irin wannan abubuwan sun yi yawa a kasuwa.”
Ya ce, akwai abubuwa da dama da suka jawo wannan matsala kamar a shekarun baya a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, an yi gyaran tashoshin jiragen ruwa, a lokacin sai aka cire mutane da tashoshin ruwa don ba wa mutane damar shigo da kayansu da sauki, to a lokacin an hana hukumarsu tantance ingancin kayayyakin da ake shigo da su abin da ya janyo aka rinka shigar da kaya marassa inganci.
Shugaban hukumar tabbatar da ingancin kayayyakin ya ce ”a wasu lokuta idan muka tare motocin da suka yi dakon kaya musamman kayan da aka dauko daga tashoshin jiragen ruwa, wani lokaci mu yi sa’a mu kama mutane da suka dauko kaya marassa inganci”
Ya ce “Amma a wasu lokuta saboda yawancin mutanen da suka shigo da kayan basu da gaskiya, idan aka tare motocin dakon kayan na su sai kaga sun yi amfani da bindigogi ko wukake sun kori ma’aikatan hukumar”
Malam Farouk Ali Salim, ya ce “Idan kuma aka kai kayayyakin zuwa kasuwanni jami’anmu suka shiga domin tantancewa sai kaga an yi ca a kan jami’an na mu an yi musu taron dangi don a hana su aikinsu.”