fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yawancin tsaffin gwamnonin PDP basa iya fitowa cikin jama’a ba tare da an bisu da Jifa ba>>Adams Oshiomhole

Tsohon gwamnan jihar Edo wanda kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC ne, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa, yawancin tsaffin gwamnonin PDP basa iya shiga cikin jama’a saboda tsoron jifa.

 

Ya bayyana hakane a yayin da aka yi gawa dashi a gidan talabijin na Channelstv inda yake bugun kirji kan yanda yake da samun karbuwa a wajen jama’ar jiharsa.

Yace shin kaga yanda mutane suka tarbeni a wajan yakin neman zabe? Yace amma da yawan tsaffin gwamnonin PDP bama a jihar kadai ba ba zasu iya shiga cikin jama’a ba saboda tsoron jifa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.