Kungiyar malaman kwalejojin ilimin ta tarayya, (COEASU) ta tsunduma yajin aiki kamar yanda kungiyar malaman jami’a ta ASUU yanzu haka ke yajin aikin.
Shugaban kungiyar Malaman, Dr. Smart Olugbeko ne ya bayyana haka inda yaje yajin aikin na na gargadi ne kuma na wata daya.
Itama dai kungiyar ASUU tun a watan Fabrairu ne ta fara nata yajin aikin.
Kungiyar ta Kwalejojin ilimi tace tana son a biya mata bukatuntane kuma muddin ba’a biya ba, to zata shiga yajin aikin sai mama ta gani.