Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baiwa kungiyar kasashen Africa kyautar $550,000.
Shugaban ya bayar da kudinne a matsayin gudummawar Najariya wajan gida Great Green Wall Secretariat da za’a yi saboda dumamar yanayi.
Yace Najariya ta biya bashin da ake binta na $654,291 kan maganar.
Yayi maganane ta bakin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a Abuja wajan taron kasashen dake kungiyar.
Yace dolene kasashen Africa su rika samar da hanyoyin yaki da canjin yanayi.