Magoya bayan jam’iyyar APC a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja sun baiwa hamata iska bayan da gwamna Umahi ya basu kyautar Naira Dubu 50.
Umahi ya je ofishin jam’iyyar ne dan ganawa da shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu inda suka yi ganawar sirri.
Ko da ya fito, bai tsaya amsa tambayoyin ‘ya jarida ba inda kai tsaye ya wuce zuwa motarsa, saidai magoya baya sun baibayeshi inda shi kuma anan ne ya zaro bandir din Dubu 50 ya watsa musu.
VIDEO: APC Supporters, Others, Fight Over Umahi's N50,000 Gift
Drivers, security officials and supporters of the All Progressives Congress on Wednesday exchanged blows at the party secretariat over a cash gift from Ebonyi State Governor, Dave Umahi. pic.twitter.com/mJKgRPj5a7
— Punch Newspapers (@MobilePunch) June 2, 2022
Punchng ta ruwaito cewa, mutane sun rika dambe dan ganin sun dauki wadannan kidade da gwamna Umahi ya watsa.