fbpx
Tuesday, December 1
Shadow

Yayin da sai a shekarar 2025 za’a kammala titin Abuja zuwa Kano, a shekarar 2022 za’a kammala gadar Second Niger Bridge>>Fashola

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya bayyana cewa a shekarar 2025 ne za’a kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kano.

 

Ya bayyana hakane a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Kaduna, kamar yanda BBChausa ta ruwaito.  A wani Labarin na daban kuma mun kawo muku cewa Ministan ya dorawa ‘yan Majalisa Laifin tsawaita aikin titin da aka yi inda yace ‘yan majalisun sun nemi a mayar da titin hannu 3 shiyasa sai da suka koma suka sake shiri.

 

Saidai a bangare daya kuma Ministan yace gadar Second Niger Bridge da ake yi a jihar Delta, nan da shekarar 2022 ne za’a kammala.

 

A bayanin da yayi a wajan wani taro na masu ruwa da tsaki da wakilan jihohin Delta da Anambra,  Ministan ya bayyana cewa matsalolin rikici da kuma Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 sun kawo tsaiko wajan kammala aikin.

 

Amma yace ana sa ran nan da shekarar 2022 za’a kammala wannan gadar.

“The President asked me to assure you that nothing would stop the completion of the project in 2022.

“The project is on course; thanks to the governors of Anambra and Delta States, Willie Obiano and Ifeanyi Okowa for their efforts in returning normalcy here.

“Not withstanding, the initial conflict and COVID-19 heat, the project will be delivered as scheduled in 2022 .The President is committed to that date.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *