Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa masu rike da mukamai a gwamnatinsa dake neman tsayawa takarar siyasa a 2023 wa’adin nan da 18 ga watan Afrilu su ajiye mukamansu.
Gwamnan ya bayyana hakane ta hannun sakataren yada labaransa, Abba Anwar.
Ya kuma kara da cewa wannan ukar nasa yayi daidai da sabuwar dokar zabe me lamba 84 (12).
Hakan na zuwane yayin da shi kuma shugaba Buhari yace ba zai takurawa hadimansa masu neman mukaman siyasa a 2023 su sauka daga mukamansu ba.
Shugaba Buhari yayi dogaro da cewa sabuwar dokar zaben na cike da sarkakkiya wadda kuma tuni har kotu ta soke ta.
Saidai yace duk me neman takarar siyasa idan yana da ra’ayin sauka, zai iya sauka dan radin kansa amma ba zai takurawa kowa ba.