fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yin wasa ba tare da yan kallo ba zai taimakawa Madrid a wasan su da Manchester City>>Casemiro

Zakarun kasar sifaniyan sun sha kashi s hannun Manchester City a wasan da suka buga na 1st leg wanda suka tashi 2-1, kuma idan har madrid naso ta kai wasan quarter final to sai ta rama kwallon da City taci ta idan suka yi tafiya izuwa Ingila.

Casemiro ya gayawa Esporte Interactivo cewa za’a samu banbanci a wannan wasan nasu. Wasan zai yiwa kowa kyau kuma zai ba gabadayan su wahala. Amma sune Real Madrid kuma sun san suna da damar samun nasara a wasan saboda masoyan City baza su hallaci wasan ba hakan zai basu wata yar alfarma.
Amma sai dai yanayin wasan ba zai canja ba saboda suna da babbar kungiya kuma yan wasan dai sune kuma kochin nasu shima yana nan.
Ana ta yin maganganu akan matsayin Bale a Madrid tun shekarar data gabata, amma duk da sukar shi da ake yi Casemiro ya bayyana cewa Bale yana aiki yadda ya kamata.
Yayin da yake cewa Bale yana nan yadda yake kuma shi kan shi ya san wannan lokacin ba shine mafi kyawu ba a rayuwar shi. Amma kochin su da kungiyar kungiyar bakidaya suna taimaka mai. Bale kwararren dan wasa ne kuma yana cin kwallaye a wasan final na gasar Champions League kuma yana cikin fitattun yan wasa uku na duniya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United ne saboda Lionel Messi, karanta kaji dalili

Leave a Reply

Your email address will not be published.