fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Yuro biliyan biyu kungiyoyin firimiya lig suka kashe a kasuwar ‘yan wasan bana

Manyan gasar kwallon kafa guda biyar na fadin duniya sun kashe makudan kudade a kasuwar ‘yan wasan bana wacce aka kulle jiya ranar alhamis daya ga watan Satumba.

Inda babbar gasar kasar Ingila ta Firimiya Liga tafi kowa kashe kudi bayan data lale yuro biliyan biyu wurin sayayyar sabbin ‘yan wasa.

Sai babbar gasar Italiya ta Serie A tazo ta biyu inda ta kashe yuro miliyan 670 yayin da babbar gasar kasar kasar Jamus ta Bundesliga ta kashe yuro miliyan 435.

Ta bangaren gasar Faransa ta Lig 1 kuwa yuro miliyan 426 suka kashe yayin da babbar gasar Sifaniya ta La Liga ta kashe yuro miliyan 404.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *