Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, wanda kuma dan majalisar zartarwar babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya ne, PDP, ya ce kishin kasa da sanin hakkin shugabanci ne suka sa jam’iyyar ta ki ware wa wani bangare takarar shugabancin Najeriya ta 2023.
A wata tattaunawa da BBC ya ce, da dama ana ganin jam’iyyar ta su ba za ta kai labari ba, amma kuma yau sai ga shi ta zama da ‘yan takara ba iyaka, to wannan ya nuna cewa ashe ana son jam’iyyar.
Sule Lamido ya ce wannan ya nuna cewa PDP ta ‘yan kasa ce, masu kishin kasa, domin kasa, sabanin sauran jam’iyyu.
Tsohon gwamnan ya ce maganar da wasu ke yi ta a ba bangarensu takara, babu laifi kowa ya bukaci hakan, to amma idan kowa zai yi maganar son ransa ”to wane ne a tsakiya?”
Saboda haka hikima da basirar jam’iyyar ta su ita ce, hakkin shugabanci shi ne a tsakiya, shi suke bi da ‘yan Najeriya, shi suka yi, wanda hakan ya hana su ware wa wani bangare takarar.
Ya ce batun matakin da suka dauka zai sa ‘yan takara su yi yawa idan za a yi zaben fid da gwani, ya ce, ai hakan ya nuna cewa jam’iyyar ta su tana da farin jini.
Ya ce bayan sun fadi zabe lokacin da Buhari ya hau mulki, kusan duk arewa ma ba PDP, saboda an firgita su, sun ji tsoro: ” An wulakanta mu an ce mai gudu ya gudu, Buhari ya zo mai kaza, duk an yi wannan hayaniyar, an firgita mu, har ma kusan mu kanmu muna shakkar kanmu.”
Ya kara da cewa: ”Mu din nan an kona mana wurin aikinmu, wasu an kona gidajensu, wasu sun mutu. Saboda haka wannan jam’iyyar ce fa da aka ce ta firgita, aka fara ganin ‘yan takara ba iyaka.”
”Ke nan wannan shi yake nuna cewa ashe ana son jam’iyyar” in ji shi.
Babban jigon a PDP ya ce maganar da wasu ke yi cewa suna dabara ne domin sanin bangaren kasar da jam’iyya mai mulki ta APC za ta mika takarar zaben na 2023, kafin su fitar da tasu matsayar, sai ya nuna cewa idan ma haka ne to ai ba laifi domin abu ne da yake kamar yaki wanda kowa zai yi abinsa cikin sirri domin kaiwa ga nasara.
Wannan ne ya sa a Najeriyar ake daukar, manyan jam’iyyun, APC mai mulki da kuma PDP babbar jam`iyyar hamayya, na ci gaba da yi wa juna ɓad-da-bami game da maganar karɓa-karɓar shuganacin kasar..
Ko a zaman da majalisar zartarwar jam’iyyar ta PDP ta yi ranar Laraba, an yi tsammani za ta fadi yankin da ta kebe wa takarar shugaban kasa, amma ta bar takarar a bude.
Zuwa yanzu sama da mutane goma ne suka bayyana aniyarsu ta neman yi wa jam’iyyar ta PDP takarar shugabancin Najeriyar a zaben da za a yi a 2023.
Kuma hudu daga cikin gwamnoni 19 na jam’iyyar na daga cikin masu nema, hadi da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.