fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

 

Ƙasashen Afirka ta Kudu da Amurka za su fara gwajin riga-kafin cutar HIV, inda suka yi kira ga mutane da su bayar da haɗin kai domin gudanar da gwajin.

 

Cibiyar bincike ta Amurka (NIH) ta ce an ƙirƙiri sabon riga-kafin mai suna VIR-1388, domin taimaka wa ƙwayoyin jini masu taimaka wa garkuwar jiki da ake kira ‘T-cells’, waɗanda ke yaƙar sauran ƙwayoyin cutuka da ke kawo wa jiki hari.

 

Riga-kafin zai taimaka wajen sanya garkuwar jiki ya samar da ƙwayoyin ‘T-cells’, waɗanda za su iya gano ƙwayar cutar HIV domin sanar da garkuwar jiki, don ya ɗauki matakin kare jiki daga mummunar illar da ƙwayar za ta yi wa jiki.

 

Cibiyar bincike ta Amurka NIH, da gidauniyar ‘Bill and Melinda Gates’ da wani kamfanin Amurka mai suna Vir Biotechnology ne suka ɗauki nauyin gwajin riga-kafin.

Karanta wannan  Shugaba Tinubu zai kashe Naira Miliyan Dari biyu wajan ciyar da dabbobin dake Aso Rock

 

Za a gudanar da gwajin ne kan mutum 95 da ba sa ɗauke da cutar a wurare huɗu a Afirka ta Kudu da kuma wuri shida a Amurka.

 

Ana sa ran sanar da sakamakon farko na gwajin a ƙarshen shekarar 2024, amma za a ci gaba da gudanar da gwajin kan mutanen har zuwa shekaru uku masu zuwa.

 

A shekarar 2020, Cibiyar NIH ta dakatar da gwajin wani riga-kafin HIV a Afirka ta Kudu bayan da aka gano cewa riga-kafin baya hana haɗuwar cutar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *