fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Za a kara kudin aikin Hajji da kashi 50 cikin 100 a bana a Najeriya

Hukumar alhazai ta kasa a Najeriya NAHCON ya ce da dukkan alamu za a kara kudin aikin Hajji da akalla kashi 50 cikin 100 daga wanda maniyata suka biya a 2019.

jaridar Daily Trust ta ce a 2019 maniyata sun biya naira miliyan 1.5 ne, saboda haka wadanda suka ajiye kudin guzuri tare da hukumar NAHCON na bukatar kara biyan kimanin naira miliyan 1 ke nan.

Yayin wani taro da hukumar ta yi da jami’an da ke kula da hukumomin aikin Hajji na jihohin Najeriya, shugaban NAHCON Alhaji Zikrullah Hassan ya ce hauhawar farashi ga tattalin arzikin duniya ne ya janyo wannan matsalar.

Karanta wannan  Hotunan yanda wani dan Achaba ya dauki yaran makaranta da yawa ya dauki hankula

Ya ce a shekarar 2019, a na sauya dalar Amurka daya kan Naira 306, inda a bana ya koma Naira 410 kan kowace dala.

Y abayyana cewa kashi 97 cikin 100 na kudaden aikin Hajji na tafiya ga biyan ayyuka da ake biya da kudaden waje ne kamar sayen tikitin jirgi da na masauki a kasa mai tsarki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.