fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Za a yi wa Ali Nuhu da ‘yan Kannywood 5 gwajin coronavirus

Tauraron fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya ce hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya za ta yi masa gwajin cutar coronavirus.

 

 

Ali Nuhu da wasu ‘yan Kannywood biyar na cikin taurarin da suka halarci bikin karrama jarumai da aka gudanar a Lagos ranar Asabar 14 ga watan Maris.

 

 

Gwamnatin jihar ta Lagos ta yi kira ga duk wanda ya halarci bikin ya je a yi masa gwajin coronavirus saboda ta gano cewa wani mai dauke da cutar ya halarci bikin.

 

 

Za a samu sakamako ranar Laraba

A hirar da ya yi da BBC ranar Talata da daddare, Ali Nuhu, ya ce jami’an hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya sun je wurinsa inda suka bukaci ya bi su ofishinsu domin yi masa gwajin cutar ta coronavirus.

 

 

Kazalika ya ce sun je wurin sauran abokan sana’arsa da suka halarci wurin bikin karrama taurarin.

Karanta wannan  Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

 

Sauran ‘yan Kannywood din da suka je Lagos domin halartar bikin su ne: Ado Gwanja da Abubakar Maishadda da Hassan Giggs da kuma wani mutum daya.

 

 

A cewar Ali Nuhu, za a gudanar da gwajin ne a daren nan sannan a gaya musu sakamakonsa ranar Laraba.

 

 

Ya zuwa yanzu dai fiye da mutum 40 ne suka kamu da cutar, ciki har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari da kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

 

 

A karon farko tun bayan barkewar cutar a Najeriya, an samu mutum daya ya mutu sanadiyyar ta ranar Litinin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *