fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Za a ceto dukkan yaran da ke hannun Boko Haram>>Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da kokarin ganin ta ceto dukkan sauran raya da Boko Haram ke ci gaba da yin garkuwa da su.

Buhari ya yi wannan albishir ne Birnin Addis Ababa, a wurin Taron Kare Rayuwar Kananan, wanda ta shirya tare da Norway, Uganda, Sudan, Tarayyar Turai da kuma kungiyar Ceton Kananan Yara, wato ‘Save The Children’.
Buhari ya ci gaba da yi wa mahalarta taron bayanin cewa, ‘Najeriya ta ceto wasu yaran da aka yi garkuwa da su daga a Chibok da Dapchi. Mu na kan kokarin ganin an ceto dukkan sauran wadanda har yanzu ke tsare a hannun ‘yan Boko Haram.”
“Guyawun mu ba za su taba gajiyawa ko nuna sarewa ba, har sai mun tabbatar cewa mun ceto dukkan yaran da ke hannun ‘yan ta’adda”
Ya kuma yi kira ga kasashen wannan hadin guiwa da a tashi tsaye a kawar da illar take hakkin kananan yara da a yanzu ke kara munana da kamari a cikin duniya.
Buhari ya gode wa Sojojin Hadin Guiwa na Kasa-da-kasa bisa gagarimar gudummawar da su ke bayarwa wajen kokarin dakile ta’addanci.
Ya kuma yi dogon bayani game da nasa’orin da gwamnatin sa ta samu wajen yaki da ta’addanci da kuma hana take wa kananan yara hakkin su.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Bidiyo; Ya kamata mahukuntan Najeriya su fahimci cewa, indai za'a taba Janibin Manzon Allah, Annabi Muhammad(SAW) to matasa basu jiran ace musu ku yi ko kar ku yi


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.