fbpx
Monday, June 27
Shadow

Za mu gabatar da Magu gaban kotu nan gaba>>Ministan ‘yansanda

Ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Maigari Dingyadi, ya ce mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu zai gurfana gaban kotu ne kawai idan an kawo rahoton binciken da ake gudanarwa a kan shi da mai shari’a Justice Ayo Salami-led ke jagoranta.

Ya bayyana haka ne a jiya ya yin taron ministoci na mako-mako wanda tawagar ‘yada labarai na shugabancin Najeriya a Abuja.

A watan Yulin 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wata tawaga da za ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Magu, biyo bayan koken da Antoni Janar na kasa ya shigar Abubakar Malami.

Leave a Reply

Your email address will not be published.