fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Za mu iya hukunta shi – Shugaban jam’iyyar APC ya yi magana a kan zazzafan kalaman Tinubu ga Shugaba Buhari a Abeokuta

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyar ba ta ji dadin zazzafan kalaman daya daga cikin masu neman shugabancin kasar nan ba, Bola Ahmed Tinubu kan Shugaba Buhari a Abeokuta, a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni.

Yayin da yake magana da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja a ranar Asabar, 4 ga watan Yuni, Adamu ya ce mai yiwuwa a sanya wa Tinubu takunkumi.

Idan baku manta ba, Tinubu yayin da yake neman goyon baya a zabe mai zuwa a Abeokuta lokacin, ya ce ya cancanci a mara masa baya duba da irin yadda ya taimaka wa Shugaba Buhari ya ci zaben 2015. Saidai da dama dai na kallon jawabin nasa a matsayin rashin mutuntawa ga shugaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.