fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Za mu kammala titin jirgin ƙasa na Kano-Kaduna zuwa Disambar 2022>>Amaechi

Gwamnatin Taraiya ta baiyana yaƙinin ta na kammala titin jirgin ƙasa na Kano-Kaduna a Disambar 2022.

Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ne ya baiyana haka yayin duba yanayin aikin a Kano.

A cewar sa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne zai ƙaddamar da aikin kafin ya bar mulki.

Amaechi ya baiyana cewa gwamnatin taraiya ta kashe sama da dala miliyan 400 domin samar da aikin.

Ministan ya yi kira ga kamfanin da ya ke yin aikin, CCECC da su ƙaro kayan aiki da ma’aikata domin cimma wa’adin kammala aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.