fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Za mu rama idan aka kori makiyaya daga kudu – kungiyar Fulani

Farfesa Umar Labdo shi ne Babban Sakataren Kungiyar Raya Fulanin Najeriya, FULDAN sannan kuma Farfesan Tunanin Siyasar Musulunci a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano. A wannan tattaunawa da yayi da manema labarai, ya bayyana cewa, ya gano asalin rikicin makiyaya da manoma a kasar nan kuma ya kawo mafita kan yadda za a samu zaman lafiya a kasar.

Farfesa Labdo yace bai kamata a dinga dangata ta’addanci da wata kabila ba, saboda babu kabilar da babu masu aikata laifuka a cikin ta.

Farfesa Labdo ya bada misali, Inda yace ana danganta yarbawa da harkar damfara ta yanar gizo, Ibo kuma ana alakanta su da safarar miyagun kwayoyi sai kuma fulani da ake dangatawa ta’addanci yan bindinga.

Farfesa Labdo yace tabbas mafi Yawanci yan bindingar da aka kame fulani makiyaya ne, amma ba hakan yana nufin duk kabilar yan ta’adda bane.

Yace hanyar da za abi don magance rikicin makiyaya da manoma shine, Gwamnatin ta baiwa makiyaya isassun dazukan kiwo, buda masu cibiyoyin Kiwon lafiya da sauran abubuwan more rayuwa.

Sannan duk fulanin da ya saba doka a hukunta daidai da abunda ya aikata, amma ba wai a kori fulani daga jihohin kudu ba.

A karshe ya gargadi Gwamnoni da Shugabannin yankin kudu kan korar mutanen su a yankin, idan ba haka ba su ma zasu rama ga mutanen su dake jihohin arewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *