fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Za mu yi amfani da irin dabarun kwato daliban Kankara don kubutar da daliban da aka sace a Neja>>Ministan Tsaro

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi ya ce gwamnati za ta yi amfani da irin dabarun da ta yi amfani da su wajen kubutar da yaran makarantar Kankara don ceto dalibai 27 da aka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara, jihar Neja a yau 17 ga Fabrairu.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen shirin tantance shugabannin hafsoshin da Majalisar Wakilai ta fitar a yau 17 ga Fabrairu.

Ya ce shugabannin hafsoshin za su fara aiki kai tsaye da bayan yan majalisar sun tantance su, zasu bi sawun masu satar mutanen da nufin kubutar da yaran.

Ya kara da cewa har yanzu basu samu rahotannin ba kan ayyukan da ke gudana a Jihar Neja ba.

Amma na tabbata kafin karshen ranar, za a ba mu cikakken bayani kan abin da ke faruwa a Jihar Neja ”in ji Magashi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *