A ranar 17 ga watan disemba za’a gudanar da tseren gudu na Marathon a babban birnin tarayya Abuja, cewar wa’yanda suka tsara tseren.
Shugaban kungiyar data tsara tseren, Femi Abegunde ne ya bayyana hakan ranar talata,
Kuma yace mutane 60 ne zasu yi wannan gasar hadda ‘yan kasar waje ma zasu shiga a fafata dasu.
Yayin da za’a baiwa wanda ya lashe gasar kyautar dala 80,000 wanda yayi daida da naira 48,800,000.
Kuma za ayi gudun ne na kilo meter 42 fadin babban birnin tarayyar.