fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Za’a cigaba da buga wasannin gasar Bundlesliga ranar 16 ga watan mayu

Hukumar wasannin kasar jamus DFL ta sanar cewa za’a cigaba da buga wasannin gasar Bundlesliga ranar 16 ga mayu, yayin da aka dakatar da wasannin tun a watan febrairu.

Shugaban DFL Christian Seifirt shine ya tsara yadda za’a cigaba da buga wasannin, yayin da zasu buga wasanni shida a ranar sati wanda suka hada da Dortmund da Schalke da dai sauran su.
Zasu gama tsara ranakun wasan nasu ne a ranar litinin 18 ga wannan watan.
A ranar laraba gwamnatin kasar ta sanar cewa za’a cigaba da buga wasannin gasar Bundlesliga a tsakiyar watan mayu idan har kunyoyin wasan suka bi dokokin da aka tsara masu.
Bayern Munich sune a sama teburin gasar yayin da suka kerewa abokan hamayyar su Dortmund da maki hudu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan wasan Manchester sun bukaci a sayar da Ronaldo kuma har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar

Leave a Reply

Your email address will not be published.