fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Za’a daure mutum har tsawon shekaru 3 idan bai saka takunkumin rufe baki da hanci ba a kasar Qatar

Kasar Qatar ta saka dokar amfani da takunkumin rufe baki da hanci ya zama dole inda tace duk wanda aka kama da laifi zai yi zaman gidan kaso na shekaru 3 ko kuma ya biya diyyar Riyal 200,000 wanda yake daidai da Dalar Amurka 53,000.

 

Ministan harkokin cikin gida na kasar ne ya bayyana haka inda yace dokar zata fara daga Ranar Lahadi me zuwa, 17 ga watan Mayu.

 

Saidai yace wanda kawai za’a kyale ba lallai sai sun saka takunkumin rufe baki da hanci ba shine idan aka ga mutum na tuki shi kadai a cikin mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published.