Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha na can tsare a ofishin ‘yansanda inda ake tuhumarsa da balle rukunin gidajen Royal Palm Estate da gwamnatin jihar ta kulle.
Rukunin gidajen mallakin matar tsohon gwamnan ne kuma a yayin da ya je balleshi an samu arangama tsakaninsa da mutane bangaren gwamna Hope Uzodinma inda har aka lalata motocinsa.
Wata majiya daga hukumar ‘yansanda ta sanar da Vanguard cewa a gobe za’a gurfanar da tsohon gwamnan a Gaban Kuliya.