Sunday, June 7
Shadow

Za’a ragewa Messi da Ronaldo albashi amma duk da haka zasu cigaba da karbar albashi mafi tsada a tsakanin yan kwallo

An dakatar da wasannin kwallon kafa da dama a nahiyar turai saboda barkewar cutar coronavirus/ Covid-19. kuma hakan yasa kungiyoyi da dama suna fama da rashin kudi har ta kai ga suna rage albashin yan wasan su.

 

Zakarun kwallon kafa Ronaldo da Messi zasu yi babban rashi idan aka rage albashin. Kuma kwanan nan za’a tilasta masu karbar ragin albashin.

 

An samu labari cewa Barcelona sun fi kowane kulob kudi a nahiyar turai. Kuma duk da cewa zasu rage albashin yan wasan su Messi zai cigaba da daukar albashi mafi tsada a tsakin yan kwallo amma banda abokin hamayyar shi Ronaldo.

 

Kungiyar juventus zata rage kashi 30 bisa dari nadaga albashin yan wasan su kuma hakan zai sa yan wasan su rasa kimanin dala miliyan 20.

 

A kowace shekara Messi yana samun albashin dala miliyan 145 amma yanzu zai karbi dala miliyan 78. Ronaldo kuma yana samun dala miliyan 130 amma yanzu zai karbi dala miliyan 91.
Ragin albashin da kungiyoyin zasu yi zai fi shafar Neymar akan Messi da Ronaldo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *