Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta ce ba za ta kara wa’adin daga ranar 26 ga watan Maris ba don yin rajistar jarrabawar gama-gari ta 2022 (UTME) da Direct Entry (DE).
Magatakardar JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ake sa ido kan rajistar a Cibiyar Koyon Kwamfuta ta Duniya a jiya a Abuja, ya ce ba za a kara wa’adin ba saboda hukumar na aiki da “tsattsauran jadawali”.
Oloyede ya nuna rashin jin dadinsa yadda yaga mutum daya a cibiyar akayi wa rajista, maimakon 200 ko fiye da aka saba yi a kowace rana.