fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Za’a yi kidayar ‘yan Najeriya a watan Mayu

A karon farko cikin shekara 15, za a yi ƙidayar ‘yan ƙasa a Najeriya, a cewar shugaban hukumar ƙidaya ta ƙasa National Population Commission.

Nasir Isa Kwarra ya ce fasahar zamani za ta taimaka wajen tabbatar da cewa an gudanar da sahihiya kuma karɓaɓɓiyar ƙidaya da ake sa ran gudanarwa a watan Mayu mai zuwa.

Wasu daga cikin ƙungiyoyin kudancin Najeriya ba su yarda da sakamakon ƙidayar da aka yi ba a 2006, suna masu zargin maguɗi don fifita yankin arewaci.

Ƙiyasi ya nuna cewa al’ummar Najeriya sun kai miliyan 200, idan aka kwatanta da miliyan 140 da aka samu a 2006.

Karanta wannan  So makaho ne: Wata matashiya 'yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin sahibinta mai dauke da cutar kanjamau

Sai dai ana jiran Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da takamammiyar ranar da za a fara ƙidayar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.