Gwamnan jihar kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa zabar Kashim Shttima da Asiwaju Bola Ahmad yayi yayi daidai.
Ya bayyana hakan ne ta hannun wasikar data fito daga hannun kwamishinan sadarwa na jihar Kano, Garba Muhammad.
Kuma ya bayyana ne bayan dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC, Tinubu ya zabi Shettima a matsayin abokin takararsa ranar lahadi.
Kuma yace zabar tsohon gwamna jihar Bornon daya yi ya nuna cewa APC ce zatayi nasarar lashe zabe mai zuwa.