Dan takarar Jam’iyyar APC na shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu na shirin zabar Musulmi dan uwansa a matsayin abokin takara amma kungiyoin Kiristocin Najeriya sun kalubalanci hakan.
Inda sukace ba a yiwa Kiristoci adalci ba kamata yayi a hada Musulmi da Kirista ba Musulmi da Musulmi ko kuma Kirista da Kirista ba.
Amma sanata Orji Kalu yace masu su kwantar hankulansu domin matar Bola Ahmad Tinubu fastuwa ce, saboda haka kar su damu.
Sanatan ya kara da cewa shi kanshi matar shi ce shugaba a gidansa, kuma kowama hakane saboda mata itace ke baiwa mai gidanta shawara. Saboda haka Kirista su kwantar da hankulansu ba zata taba bari a cuce su ba.