fbpx
Friday, October 23
Shadow

Zaben Edo:Suna tafka min Magudi>>Gwamna Obaseki ya koka

Gwamnan jihar Edo wanda kuma shine dan takarar PDP a zaben gwamna dake gudana a yau ya koka da cewa ana tafka masa magudi a zaben.

 

Gwamnn ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Crusoe Osagie inda yace abin mamaki inda yake da masoya dayawa sai ake cewa wai na’urar tantance masu zabe ta daina aiki.

Ya bada misalin Oredu 1,Unit 2 inda yace irin haka ya faru, yace kamata yayi INEC ta nunawa Mutanen Edo cewa zata iya gudanar da zabe na gaskiya.

 

Ya kara da cewa da gangan ake hana mutane su yi zabe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *