fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

ZABEN 2023: Idan Muka Yi Sake Atiku Zai Iya Cin Banza, Cewar Kwankwaso

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Tsohon gwamnan jihar kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace idan har haduwar su da Peter Obi bata yiwu ba to da alamar Atiku Abubakar yaci banza a zaben 2023.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce akwai wasu ‘yan hana ruwa gudu a wajen maganar hada-kai da ‘Yan LP

Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa yana sa ran Peter Obi ya zama abokin takararsa a zabe mai zuwa Idan dunkulewar NNPP da LP ta gagara, watakila Jam’iyyar ta ba Kingsley Moghalu tikitin mataimakin shugaban kasa.

Har yanzu, Rabiu Musa Kwankwaso yana sa ran cewa akwai yiwuwar a samu fahimtar juna tsakanin New Nigeria Peoples Party da jam’iyyar LP.

A hirar da aka yi da tsohon Gwamnan Kano, kuma ‘dan takarar shugaban kasa a NNPP, ya tabbatar da ana kokarin ganin kansa ya hadu da na Peter Obi.

Kamar yadda Rabiu Kwankwaso ya shaidawa Channels Television a tattaunawarsu ta ranar Lahadi, wasu su na yi wa jam’iyyar LP shiga sharo babu shanu.

Karanta wannan  Ahmad Lawal da hafsoshin tsaro sun tashe tsaye don kare tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari

Inda za a shawo kan lamarin shi ne a samu mutanen da suka cancanta daga bangaren jam’iyyar LP da Peter Obi, ayi magana, la’akari da duba halin da ake ciki.

Majiyar mu ta jiyo mana cewa Kwankwaso yana cewa babbar matsalar da suke fuskanta a kan hadin-kan, shi ne wanda za a ba tikitin takara.

Shi dai ‘dan takaran na NNPP Kwankwaso ya ce yana yi wa mutanen kudu maso gabas kwadayin su samu mulki domin a rika damawa da su, tun da an yi watsi da su.

“Ina da dalilai da suka sa na ke tausayin Kudu maso gabas, ina tunanin cewa hadin-kan NNPP da LP zai rage tashin hankalin da ake ciki a Kudu maso gabas.

Daga Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.