fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Zaben 2023: PDP tana tantance ‘yan takarar shugaban kasa

A ranar Juma’ar nan ce jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta soma tantance masu son tsaya mata takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Bayanai sun nuna cewa babbar jam’iyyar adawar za ta tantance mutum 17 da ke fafatawa domin ganin sun tsaya mata takara a zaben shekara mai zuwa.

Ana gudanar da tantancewar ce a ofishin jam’iyyar mai suna Legacy House, da ke unguwar Maitama, a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Jam’iyyar ta PDP ta sanya Naira miliyan arba’in a matsayin kudin fom na takarar shugaban kasa.

Mutanen da ke son yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa sun hada da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar; gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Kazalika akwai gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike; gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel; tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki.

Haka kuma akwai tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim.

Tuni dai Atiku Abubakar da Sanata Saraki suka wallafa sako a shafinsu na Facebook suna masu cewa an tantance su.

Tun a farko mako ne jam’iyyar ta soma tantance masu son tsaya mata takara a sauran mukamai da suka hada da gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin tarayya da jihohi.

Daya daga cikin jami’an da jam’iyyar ta aika jihar Kaduna, Alhaji Yusuf Dingyadi ya shaida wa BBC cewa tantancewar “za ta hada da duba shaidar kammala karatun masu son tsayawa takara, da rasiti na biyan haraji da kuma shaidar cewa mutum yana hidimta wa jam’iyyarmu.”

PDP za ta tantance ‘yan takarar ne kwanaki kadan bayan wata hadaka ta masu neman tsaya mata takara daga arewacin kasar ta wargaje.

Hadakar, wacce ta kunshi Sanata Bukola Saraki da gwamnan Bauchi Bala Mohammad da gwamnan Sokoto, Aminu Waziru Tambuwal da Muhammad Hayatudeen ta wargaje bayan gaza yin maslaha a tsakaninsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.