Tsohon shugaban kasa Janar Olusegun Aremu Obasanjo ya ayyana dan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyar PDP Dr. Ugo William a matsayin dan takara nagartacce wanda ya kitsa domin ceto kasar nan daga halin da take ciki.
A cigaba da bayyana yan takarar da ke son fitowa takara, a kakar zabe mai zuwa, musannan matasa, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya shawarci matasa da su hada kansu domin ceto kasar nan. Domin matasa sune kashin bayan cigaban kowace al’umma.
Dr. Ugo William matashi ne da yake neman jam’iyyar PDP ta ba shi tikitin takara a zabe mai zuwa na shekarar 2023.


Obasanjo ya ayyana hakan ne lokacin da Dr. Ugo Williams ya ziyarce shi domin tattaunawa akan batun takarar shi.
Obasanjo ya shawarci matashin da ya zagaya sauran yankuna na Nijeriya domin neman goyon bayan matasa ‘yan uwansa.
Rariya.