A karamar hukumar Sandamu dake jihar Katsina an sami mutum biyu ‘yan gida guda wanda suke uba daya sun fito takara a mazaba guda kuma a jam’iyya guda.

Alhaji Suraja Sani Manzo shine dan majalisar jiha wanda a yanzu haka kaninsa Alhaji Mustapha Sani Manzo yake neman kujerar tasa kuma dukkanninsu kowa ya sayo fom din tsayawa takarar.
AN CE SIYASA BADA GABA BA, AMMA ITA WANNAN KAMAR TAZO DA GABAR.
Daga Sale Lawal Sandamu