fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Zaben fidda gwani na APC:”Kun bani kunya kuma ba zan kara amincewa daku ba”>>Gwamna Umahi ya fadawa Ohanaeze Ndigbo

Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya caccaki kungiyarsu ta inyamuran Najeriya, watau Ohanaeze Ndigbo biyo bayan kammala zaben fidda gwani na APC.

Inda yace ‘yan kungiyar sun bashi kunya domin sun kasa sasantawa da Deliget din jijohinsu guda biyar dake Najeriya.

Tsohon dan takarar shugaban kasan a jam’iyyar APC ya kara da cewa ‘yan kungiyar sun ci amanarsa saboda haka ba zai kara yarda dasu ba.

Gwamna Umahi yayi wannan jawabin ne a Uburu dake jihar Ebonyi ranar asabar, inda a karshe yace yaji matukar kunya saboda yadda deliget dinsu sukayi zaben fidda gwani na APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published.